Cikin Jarirai mil 13.4 Da Ake Haifa Duk Shekara Mil Daya Suna Mutuwa

Jariri

Kusan jarirai miliyan daya ne suke mutuwa a kowace shekara, bisa dalilan da suka shafi yanayin haihuwarsu bakwanni, kana, an gano cewa babu wani saukin da aka samu game da lamarin a fadin duniya baki daya cikin shekaru goma da suke wuce daga shekara to 2010 zuwa 2020.

A ranar Talata ne hukumar Unicef Tare da hadin gwiwar kawayenta, ta fitar da wani rahoton da yake nuni da cewa, kimanin jarirai bakwani miliyan 13.4 da aka haifa a shekara ta 2020, kusan miliyan daya cikinsu sun mutu sanadiyyar matsaloli da suka shafi kasancewarsu bakwanni.

Rahoton da Kungiyar BORN TOO SOON, wata kungiya da take bibiyar alkaluman jarirai da ake haifa bakwanni ta jagoranta wanda ta yi wa taken “shekaru goma na daukan matakai akan haihuwar bakwanni, kulawar gaggawa kan mai kisan sari ka noke, wanda ya ke sanadin daukar rayukan miliyoyin ‘yan jariran da ake haifa kafin lokacinsu yana bukatar daukan matakai bil hakki da gaskiya domin inganta lafiya da rayuwar yara.

Rahoton, wanda ya samu hadin gwiwar kungiyoyi kamar su Unicef wato Asusun Tallafa Wa Yara Na Duniya da Kungiyar Lafiya ta Duniya WHO da partnership for Maternal, Newborn and Child Health (PMNCH), ya zayyana dabarun da za a iya amfani da su wajen shawo kan al’amarin.

Kasashen kudancin Asiya da yankin Hamada na Afirka ne suke kan gaba wajen haihuwar yara bakwanni da kiyasinsu ya kai kaso 65% cikin dari da ake samu a fadin duniya.

Wayansu yara a wani shirin UNICEF

Rahoton ya kuma yi la’akari da dalilan da suke tasiri ta yadda suke sanya rayuwar mata da jarirai cikin hadari a ko ina.

Misali anyi kiyasin cewa gurbattacen iska yana bada gudun mawa wajhaihuwar yara bakwanni a haihuwar bakwanni miliyan 6 a kowace shekaru.

Yanzu kuma ana samun karuwar wannan lamari a sakamakon Covid-19, sauyin yanayi, bazuwar tashe-tashen hankula da kuma yanayin tsadar rauwa. A cewar babar Darektar PMNCH Helga Fogstad wacce ta ce “babu wani cigaba da ake samu a fannin lafiyar jarirai da ake Haifa dakuma kiyaye haihuwar jarirai bakwanni.”

Rahoton ya kuma gano cewa babu wani sauyi da aka samu a sassan duniya baki daya cikin shekaru goman da suke wuce akan haihuwar jarirai bakwanni inda kimanin jarirai miliyan 152 suka kasance cikin hadarin yiwuwar haihuwarsu kafin su gama kosawa a cikin daga sheka ta 2010 zuwa 2020.

Su dai bakwanni, ana haihuwar su ne yayin da mace tayi tsawo makonni 37 tana rainon ciki sabannin tsawon makkonni 40 da ya kasance lokacin da ya dace haihuwar jarirai.