Ciki Da Gaskiya: Tsoffin ‘Yan Sanda Da Suka Bautawa Najeriya Tsawon Rayuwar Aikinsu Na Neman Hakkinsu Bayan Ritaya, Maris 06, 2023

Sarfilu Hashiim Gumel

Sabon shirin ya duba korafin wasu jami’an ‘yan sanda da su ka share yawancin shekarun su su na aiki a Maiduguri jihar Borno, musamman ma lokacin da a ka samu illar ‘yan Boko Haram.

Kamar wasu takwarorin su a wasu yankuna, ‘yan sandan sun ce sun yi aiki na tsawon shekaru 35 inda su ka yi ritaya a 2018.

Sun tinknari shirin CIKI DA GASKIYA su na masu cewa kudin karin albashi da a ka yi mu sun a tsawon wata 8 sun makale kuma yanzu sun zama ‘yan fansho inda karfin su ya kare ga dawainiyar gida da yara a makaranta.

Amma, shugaban kwamitin yan sandan na Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Halliru Dauda Jika, ya sha alwashin duba batun da zarar Majalisa ta koma aiki bayan zabe:

Ayi sauraro lafiya:

Your browser doesn’t support HTML5

Ciki Da Gaskiya: Tsoffin ‘Yan Sanda Da Suka Bautawa Najeriya Tsawon Rayuwar Aikinsu Na Neman Hakkinsu Bayan Ritaya - 11"03"