Washington DC —
Sabon shirin ya waiwayi batun dan kasuwar harkar man fetur din nan, Muhammad B. Alhassan daga jihar Nasarawa, wanda tun kimanin shekaru 7 kudin sa da su ka kai tiriliyoyin Naira, su ka makale a bankuna da hakan ya maida shi tamkar mai gararamba kan titunan Abuja, don har na cefane ma yakan nema ya rasa.
Amma bayan gwagwarmaya da taimakon kungiyoyin kare hakkin Bil Adama, yanzu banki ya bashi takardar kotu da ke nuna cewa gwamnatin Najeriya ce ta nemi a dakatar da kudaden.
Saurari shirin: