A cikin hirarsu da Muryar Amurka, wani dan jarida yace, duk da matsalolin ga gwamnatin ta gada daga gwamnatin da ta shude, an sami ci gaba. Bisa ga cewarsa, gwamnati ta gaji bashin albashin watanni shida da gwamnatin da ta shude bata biya ba, banda haka kuma, matasa suna zaune a gida da dama babu aikin yi. Wadansu matsalolin kuma bisa ga cewarshi, sun hada da hanyoyoyi da aka fara gyara a wurare da dama amma ba a kamala ba, banda matsalar tsaro da suka shafi rikici tsakanin Fulani da kabilar Berom a kanannan hukumomin Riyom da Barikin Ladi.
Daya daga cikin nasarorin da gwamna Lalong ya samu bisa ga cewarshi, sun hada da zaunawa da kabilun dake rikici da juna domin neman hanyar da za a sami masalaha.
A cikin wata hira da Muryar Amurka gwamna Lalong yace batutuwa da zaifi maida hankali a kai sune batun zaman lafiya tare da alkawarin damawa da dukan kabilu a gwamnati.
Sai dai duk da nasarorin da gwamnatin ke ikirarin samu, jama’a na kokawa dangane da hare haren da ake ci gaba da kaiwa da asarar rayuka, suka kuma yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki matakin kawo karshen asarar rayuka da kuma bannata albarkatun gona da ake yi a jihar.
Ga cikakken rahoton da wakiliyar Sashen Hausa Zainab Babaji ta aiko daga Jos, Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5