Cibiyar raya kasashe ta Amurka zata samar da sinadarin gina jiki ga kananan yara

Wadansu yara sun samu abincin ci

Cibiyar raya kasashe ta Amurak-USAID zata samar da sinadarin gina jiki domin rarrabawa sama da kananan yara dubu saba’in.

Cibiyar raya kasashe ta Amurak-USAID zata samar da sinadarin gina jiki domin rarrabawa sama da kananan yara dubu saba’in.

Cibiyar ta bayyana haka ne a karshen wani dandalin fayyace shirin da aka gudanar a Abuja da nufin shawo kan matsalar rashin abinci mai gina jiki tsakanin kanannan yara.

Manajin darektan shirin Tim Prewitt ya bayyana cewa, matsalar samun isasshen abinci wata babbar kalubala ce musamman tsakanin mata wadanda basu da wata sana’a ko abin hannu ko karfin halin tsaida shawara game da gidansu ko abincin da za a ci a gida.

Bisa ga cewarshi, sama da mutane biliyan daya, kimanin kashi daya bisa shida na adadin al’ummar duniya, suna fama da matsananciyar yunwa, yayinda rashin abinci mai gina jiki yake kashe sama da yara miliyan uku da dubu dari biyar kowacce shekara.

Ya bayyana cewa, ta dalilin haka ne, cibiyar ta ke kokarin ganin an tallafawa iyalai da basu da karfin aljihu domin su iya shawo kan matsalar rashin binci mai gina jiki da kuma talauci ta wajen koya masu dabarun noma, da sanin abinci mai arha da amfani da zasu iya ci.

Adadin kanannan yaran dake fama da rashin isassashen abinci mai gina jiki ya zarce na kasar Ethiopia, inda a jihar Kano kadai, adadin kananan yaran da suke mummunan fama da karancin abinci ya wuce na kananan yaran dake jamhuriyar Niger.