Sokoto: Cibiyar Daular Usmaniyya Za Ta Karbo Kayan Tarihin Da Turawan Mulkin Mallaka Suka Kwashe

Wasu daga cikin kayana tarihi a Daular Usmaniyya

Yanzu haka a Sokoto cibiyar Daular Usmaniya, kusan an kammala shirin tafiya Burtaniya a yunkurin dawowa da kayan tarihi na daular wadanda yanzu haka ke can kasar ta Ingila.

Wasu hukumomi a Najeriya na ci gaba da yunkurin ganin sun dawo da kayayyakin tarihi na al'adunsu da turawan mulkin mallaka suka raba su da su, lokacin da suke mulkar su.

Yanzu haka mahukunta a Sokoto cibiyar Daular Usmaniya kusan sun kammala shirin tafiya Burtaniya a yunkurin dawowa da kayan tarihi na daular wadanda yanzu haka ke can kasar ta Ingila.

Kasashen Afirka da suka fuskanci mulkin mallaka daga hannun turawa, bayan bautar da mutane, hakama sun yi hasarar kayan tarihi da al'adu da turawan suka kwasa, kuma har yanzu wasu daga cikin kayan na kasashen na turai.

Alal misali, kasar Ingila, wadda ta yi wa Najeriya mulkin mallaka, ta kwashi kayan tarihi da al'adu na al'ummomi daban-daban na Najeriya wadanda yanzu fiye da shekara 100 suna hannun turawan.

Wasu kayayyakin tarihi

Cibiyar Daular Usmaniyya na daga daulolin da suka rasa kayan tarihi da al'adu a lokacin na mulkin mallaka, inda yanzu haka mahukunta a jihar Sokoto na kokarin tafiya Ingila a kokarin dawowa da wasu daga cikin kayayyakin.

Bala Muhammad Mabera babban Darekta na hukumar kula da kayan tarihi da al'adu ta Waziri Junaidu, ya ce kusan sun kammala shirin tafiya kasar ta Ingila.

A cewarsa, za su je ne su kididdige kayayyakin Daular Usmaniya da ke kasar ta Ingila da suka hada da kayan al'adun gargajiya da rubuce-rubucen litattafan magabata domin bin hanyoyin dawowa da su Najeriya.

Babban Daraktan ya ce dawowa da su yana da amfani a wannan lokacin da kuma ga jama'ar da ke tafe a baya, haka kuma akwai litattafai masu muhimmanci wadanda Sheikh Usman Dan fodiyo da sauran magabata suka rubuta kamar wanda Abdullahin Gwandu ya rubuta akan Injiniyanci da kuma fannin kiyon lafiya wadanda za su iya yin amfani ga masu na nazarce-nazarce.

Masana tarihi da al'adu a Najeriya sun ce dawowa da kayan tarihin ana iya kallonsa ta fuskoki da dama.

Farfesa Aliyu Muhammad Bunza na Jami'ar Usmanu Danfodiyo, ya ce babu al'ummar da za ta manta da tarihinta kuma ta samu ci gaba, tarihi a cewarsa, muhimmi ne ga rayuwarmu komai ci gaban da ta samu.

Ya kara da cewa, dawowa da kayayyakin, yana da amfani sai dai kuma kar mahukunta su kwashi dukiyar al'umma mai yawa wajen dawowa da abin da amfaninsa bai kai na makudan kudin da za'a kashe ba.

Yanzu haka dai akwai dauloli da dama a ciki da wajen Najeriya da ke fafutuka akan ganin sun dawo da kayan da suka rasa ta hannun turawan da suka yi musu mulkin mallaka domin amfanin al'ummominsu.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir daga Sokoto:

Your browser doesn’t support HTML5

Cibiyar Daular Usmaniyya Za Ta Karbo Kayan Tarihin Da Turawan Mulkin Mallaka Suka Kwashe 3'15" .mp3