Ci Gaba Da Rufe Iyakan Najeriya Ya Raba Kawunan 'Yan Majalisar Dattawa

A Najeriya, har yanzu batun ci gaba da rufe iyaka da shugaba Muhammadu Buhari yayi, yana daukan hankali musamman ma a Majalisar Dattawan Kasar.

An kwashi lokaci ana mahawara a zauren Majalisar Dattawan akan batun rufe iyakar ne biyo bayan wani jawabi da Sanata Adamu Aliero ya gabatar da ke nuna muhimmancin rufewa a bisa dalilin tallafawa tattalin arzikin kasar. Wasu Sanatoci da dama sun marawa yunkurin baya a lokacin da suka amince da mahawarar.

Sanata Ahmed Babba Kaita ya bada hujjar matsalar tsaro wanda shi ne babban alhaki na Gwamnati wajen kare lafiyar rayuka, da dukiyar al'umman ta. Na biyu shi ne tattalin arziki, abu na uku kuma kasa ta samu labari cewa wasu kasashe da ke makwabtaka da kasar sun fara cin amanar ta.

Amma Sanata Kaita, yana ganin ya kamata a dauki matakin wayar da kan al'umma tukuna kafin a kaiga rufe iyakar, saboda sun san yadda za su magance matsalar da zata biyo bayan rufewar ga rayuwar su.

Jihar Borno tana cikin jihohin da ke kan iyaka da kasashe biyu, da kasar Chadi da kasar Kamaru, akan haka ne Sanata mai wakiltan Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume, ya yi korafi cewa rufe iyakar bai yimasa dadi ba, domin talakawan mazabarsa suna cikin wahala.

Ya kara bayani cewa maimakon rufe iyakar, da ma kara wa hukumomin tsaro karfi wajen inganta aiyukar su shi ne ya fi.

Wasu Sanatocin irin su Gabriel Suswan, daga Jihar Binuwai suna ganin a tattauna da kasashe da ke makwabtaka da Najeriya, tareda nuna masu hakkin kare iyakar, sanan a yawaita sintiri, da sa ido saboda hana masu fasakwari haddasa ta'asa.

A saurari cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Cigaba Da Rufe Iyakan Najeriya Ya Raba Kawunan 'Yan Majalisar Dattawa