Shugaban Amurka Donald Trump ya ce wasu magunguna biyu suna nuna alamun za su iya zama makarin cutar coronavirus da ta addabi duniya.
Yayin wani taron manema labarai da aka yi a jiya Alhamis a Fadar White House, shugaban na Amurka ya ce maganin cutar malaria da aka fi sani da "Chloroquine" a turance, wanda aka dade ana amfani da shi, ya nuna sakamako mai kyau a binciken da ake yi.
Hakan na faruwa ne a kokarin da ake yi na gano maganin cutar ta COVID-19, yana mai cewa "ba da bata lokaci ba za a gaggauta samar da maganin na chloroquine.
A cewar Trump maganin ya jima bil adama na amfani da shi, saboda haka, babu fargabar ko zai iya kashe wani, yana mai kwatantashi a matsayin maganin da zai iya "sauya al'amura."
Baya ga maganin na Chloroquine, ana kuma ganin haske akan maganin da ake kira Remdisivir, wanda aka samar da shi domin yaki da cutar Ebola, wanda shi ma Trump ya ce, hukumar kula da magunguna da abinci ta FDA a Amurka za ta yi nazari akansa.
Sai dai Kwamishinan hukumar Dr. Stepehen Hahn, ya ce, akwai bukatar a gwada amfani da magungunan a dakunan bincike kafin a fara amfani da su wajen warkar da cutar ta coronavirus.