Dalilin amincewa da karbar shugabancin shirin a Najeriya shi ne gano abubuwan da kasar ke bukata domin samun nasarar kawar da yunwa daga kasar gaba daya ta kaddamar da shiri mai dorewa.
Muradun shirin na biyu shi ne inganta ayyuka gona mai dorewa ta yadda kasa ba zata dinga dogaro ga kasashen waje ba wurin samar ma al'ummarta cimaka nan da shekara ta 2030.
Cibiyar binciken ta duniya kan aikin gona a kasashe masu zafin yanayi ita ta jagoranci kaddamar da shirin a Najeriya wanda ya hada duk masu ruwa da tsaki a harkokin aikin gona a kasar.
Tsohon gwamnan jihar Nasarawa Sanata Adamu Abdullahi kuma shugaban kwamitin ayyukan gona na majalisar dattawan Najeriya yana cikin wadanda suka gabatar da jawabi. Yace tun tsakanin watan Afirilu da Mayu na bara aka fara wannan nazarin domin a samu matsaya a inganta ayyukan noma, wato a yi kari kan abun da gwamnatin tarayya keyi.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5