Shugaban ma’aikatar harkokin kasuwanci da hukumar bincike na kasar China, Wang Hejun, ya fada a cikin wata sanarwa da yammacin Juma’a, cewa wannan harajin zai yi babban lahani ga huldan cinikayya da cibiyar kasuwanci ta duniya take kullawa kazalika zai yi mummunra tasiri a kan huldan cinikayya tsakanin kasashe.
Jami’in na China ya kara da cewa, idan har wannan matakin da Amurka ke niyar dauka ya tabbata, zai addabi muradun China kuma China zata yi aiki da kasashen da wannan lamari ya shafa don kare yancinta da muradunta.
A hali da ake ciki kuma Firayi Ministan Canada Justin Trudeau yace Canada ba zata amince da harajin da Trump ke niyar bullowa da shi a kan karafen da ake shigo dasu Amurka ba kuma yace a shirye yake ya kare masana’ntun kasarsa.