Kafar yada labarai ta kasar China ta mayar da martani akan matakin harkokin kasuwancin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka game da Chinan ta wasu hanyoyi daban.
Sailin da kasar ta China ke tir da matakin da shugaban na Amurka ya dauka , ta yi anfani da kafar yada labaran ta domin kwantar da hankulan ‘yan kasuwanta, kana ta bayyana damuwarta akan irin yadda hakan zai yi tasiri ga tattalin arzikin ta.
A shafin bayyana ra’ayin jaridar nan da ake kira PEOPLE’S DAILY,ta bayyana cewa kara kudin fito ta hannu guda kuma a bangare guda gwamnatin ta Trump tana bukatar a sasanta, wannan tamkar bayar wa da hannun dama ne kuma a karbe da hannun hagu
Jaridar taci gaba da cewa sai dai duk a karshe kasar ta China za ta yi galaba kan wannan tsarin na munafunci da Amurka ke tsarawa. Haka kuma China ba za ta mika wuya ga wannan barazanar ba.
Yanzu haka dai kwanan nan China ta kara labta wani karin harajin da yakai kashi 25 akan kayayyakin da kudin su ya kai har dala biliyan 60 na kayayyakin Amurka. Wannan mayar da martAni ne ga shirin da gwamnatin shugaba Trump ta shirya na karin kashi 25 akan kayayyakin kasuwanci na dala biliyan dari 2 na kasar China da ake shigowa dasu Amurka.