China ta haramtawa ‘yan wasan kwallon kafar kasar yin zanen tattoo a jikinsu ta kuma umarci duk wanda yake da zanen ya goge.
Hukumomin Chinar sun ce sun dauki wannan mataki ne don ya zama “abin koyi ga al’umar kasar,” kamar yadda AP ya ruwaito.
A lokuta da dama jama’a a kasar ta China kan alakanta masu tattoo da bata-gari yayin da jami’an tsaro kan yi musu kallon hadarin kaji.
Wannan sabuwar doka ta rutsa da mai tsaron gidan tawagar ‘yan wasan ta China Zhang Linpeng, wanda ya mamaye jikinsa da zanen na tattoo.
Ko da yake, ba shi kadai ba ne, domin har ila yau akwai dan wasa Shi Ke da shi ma yake da zanen a wuyansa.
Sai dai wasu da dama ba sa kallon zanen tattoo a matsayin wani abin da zai yi tasiri a jikin mutum.
Dan wasan PSG Lionel Messi da tsohon dan wasan Ingila David Beckham na dauke da zanen na tattoo.
Amma dan wasan Manchester United Cristiano Ronaldo ba shi da zanen a jikinsa.