Jiya Laraba, China ta bayyana damuwa kan shawarar da gwamnatin Donald Trump ta yanke na shirya wani haraji kashi 10, kan wani sabon rukuni na kayayyaki daga kasar kan kudi dala milyan dubu metan(200 Billion) da ya shafi dubban kayayyaki, a wani mataki na baya bayan dake kara ruruta a sabanin cinikayya, tsakanin kasashen biyu, wadanda suka fi kowace kasa bunkasar tattalin arziki a duniya.
Ma'aikatar cinikayya ta China tace ko kusa kasar ba zata lamunta da wannan mataki ba, kuma ta lashi takobin zata maida martani.
Sabon kudurin harajin, ya biyo bayan matakin farko daga Amurka na aza haraji kan kayayyaki daga China da kudin su ya kai dala bilyan 50,da zata aiwatar rukuni biyu. Wakilin harkokin cinikayya na Amurka Robert Lightizer, yace gwamnatin Trump ta yi hakurin shan yin kira ga kasar ta Sin ta daina rashin adalci ta fuskar cinikayya, kuma ta bude kasuwannin ta saboda a yi goyayya ta zahiri.
"Maimakon ta tunkari damuwar da muka nuna, sai China ta fara maida martani kan kayayyaki daga Amurka dake shiga kasar, kamar yadda ya fada cikin wata sanarwa da wakilin cinikayyar ta Amurka ya fitar wacce a ciki ya bada sanarwar sabon harajin. "Babu wani dalili na daukar wannan mataki da China tayi."