China Za Ta Cire Haraji Kan Wasu Jerin Kayakin Amurka

China ta ce za ta tsame wasu daga cikin kayakin da ake shigo da su daga Amurka daga harajin ramuwar gayya na baya bayan nan, da su ke ta sa ma juna a yakin cinakayyar da ke dada ta’azzara tsakanin kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

Ma’aikatar Harkokin Kudin China ta fitar da sunayen wasu kayaki 16 daga cikin rukunoni biyu na wasu kayaki wadanda harajin ba zai shafe su ba, ciki har da ‘yan mitsi-mitsin halittun ruwa na shrimp, da giris din kamfani, da na’uarar jinyar cutar kansa da man lausasa inji da dai sauran wasu sinadarai.

Daga ranar 17 ga wata wannan tsamewar za ta fara aiki na tsawon shekara guda.

Amurka da China sun shafe fiye da shekara guda, su na ta sa ma juna harajin ramuwar gayya, wanda hakan ya samo asali daga bukatar Shugaban Amurka, Donald Trump, da China ta yi wasu sauye-sauye a tsarin cinakayyarta, da kayan rahusa, da kuma batun harkokin kayan fasaha.