A yau Lahadi, Majalisar Dokokin kasar China, ta kada kuri’ar amincewa da shirin soke tsarin wa’adi biyu ga shugaban kasa.
Wannan mataki zai ya sa, shugaba Xi Jinping, ya ci gaba da zama akan karagar mulki har sai yadda hali ya yi.
daga cikin 'yan majalisar dokoki kusan 3,000, 2,958 ne suka amince da wannan sabon tsari.
Tsarin da kasar take shirin yin watsi da shi, kamata ya yi shugaba Xi ya kammala wa’adinsa a karshen 2023, amma masu fashin baki sun ce akwai yiwuwar ya ci gaba da shugabantar kasar.
Wannan kwaskwarima, zai iya bai wa shugaba Xi damar yin gaban kansa ta fuskar siyasa.
Hakan kuma dama ce da ba wani shugaban China da ya samu irinta, tun bayan tsohon shugaban kasar Mao Zedong da ya kafa kasar a lokacin yana mulki.
Har ila yau, soke wannan tsari na wa’adi, zai bai wa jam’iyyar kwaminsanci mai mulki, karfin iko kan gudanar da harkokin kasar, tare da zama jam’iyya kadai da aka amince ta mulki China.
Wannan sabon tsari da kasar ta China take shirin runguma na shugaban kasa ya rike mulki ba tare da wa’adi ba, yana fuskantar sukan da ba a yi tsammani ba a kasar.
Ga wasu ‘yan kasar ta China, tsarin ya tuno masu da lokacin mulkin Mao Zedong da kuma juyin-juya halin da kasar ta fuskanta shekaru aru-aru da suka gabata.