Kungiyoyin gasar Premier League biyu da za su kara a wasan karshe na cin kofin gasar zakarun nahiyar turai ta UEFA, na nuna alamu na zakuwa da wannan karawa da za su yi.
Manchester City wacce ta lashe kofin gasar Premier ta bana, za ta fafata a wasan na karshe da Chelsea.
Za a buga wasan ne a ranar 29 ga watan Mayu a kasar Portugal.
A baya an tsara za a buga wasan a kasar Turkiyya, amma saboda karuwar annobar coronavirus, aka mayar da shi kasar Portugal.
“Kwana uku ya rage……” Manchester City ta rubuta a shafinta na Twitter a ranar Laraba.
Ita dai Man City ba ta taba lashe kofin gasar ba, hasali ma, wannan ne karon farko da ta taba kai wa wasan karshe a gasar ta UEFA.
“An fara kidayar………,” Chelsea ta wallafa a shafinta na Twitter ita ma a ranar Laraba.
Ita dai Chelsea ta taba lashe kofin gasar a shekarar 2012.
Wannan shi ne karo na uku da za a samu kungiyoyi biyu daga gasar Premier da za su kara a wasan karshe na UEFA.
A shekarar 2007-08, Manchester United ta doke Chelsea, sannan a shekarar 2018-19 Liverpool ta lallasa Tottenham.
Hukumar UEFA ta bayyana cewa, ‘yan kallo 16,500 kawai za a bari su shiga filin wasan don kalon karawar ta karshe.