A ranar laraba ne Buhari ya kai ziyara Nijar kana ya dangana da kasar Chadi a ranar Alhamis domin tattaunawa da shugabanninsu kan yadda za a shawo kan matslar hare-haren kungiyar Boko Haram.
A cewar Ambasada Yufus Mamman, tsohon jakadan Najeriya a kasar Spain, kasashen Nijar Kamaru da Chadi na da matukar muhimmanci ga zaman lafiyar Najeriya.
“Akwai wani tsarin diplomasiyya wanda ya bukaci kafin ka yi nisa ka yi la’akkari da kasashen da ke makwbtaka da kai, kasashen Kamaru da Chadi da Nijar na da muhimmaci akan wannan tsari, yau in ba dan an shata kan iyaka ba da duk kasa daya ce.” Inji Ambasada Mamman.
Babban mai magana da yawun shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu ya ce da an yi sakaci kan yadda aka tafiyar da matsalar tsaron Najeriya kuma abin da ake so a yi yanzu shi ne a yi gyara.
“Alhamdulillahi an je Nijar an tattauna da shugaban su an je Chadi an tattauna da shugabansu, haka zalika Kamaru ma za a je a tattauna da su.”
Kungiyar Boko wacce ta samo asali daga Najeriya, ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu 15,000 kana ta raba mutane sama da miliyan daya da muhallansu tun daga shekarar 2009.
Hare-haren kungiyar ya kai ga har suna shiga kasashen ketare irinsu Nijar din da Chadi da ma Kamaru inda nan ma suka salwantar da rayuka tare da raba wasu mutane da dama da muhallansu.
Ga karin bayani a rahoton Hassana Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5