Ce-Ce-Ku-Ce Game Da Yawan Tafiye-Tafiyen Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari

Ana ci gaba a cece-kuce kan yawan tafiye-tafiyen da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ke, tun lokacin da ya hau kan mulki a shekarar 2015.

A daidai lokacin da wasu 'yan Najeriya ke korafe-korafe game da yawan tafiye-tafiyen da shugaba Muhammadu Buhari, ke yi zuwa kasashen duniya. Gwamnatin Buhari ta fito ta na kare kanta da cewa shugaban yana yin tafiye-tafiyen ne domin ci gaban kasa.

Kamar yadda tsohon ministan harkokin wajen Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya fada a wata hira da Muryar Amurka, ya ce tafiye-tafiyen shugabannin kasashe ya kan samar da ci gaba ga kasashensu, sai dai ana sa ra'ayin yawan tafiye-tafiyen da Buhari ya ke babu wani alfanu da ake samu, ganin yadda har yanzu kasar ke fama da wasu matsaloli.

shi kuma mai magana da yawun shugaban mallam Garba Shehu, ya bayyanawa Muryar Amurka cewa babu wani dan Najeriya da zai iya cewa babu wasu ci gaba da aka samu game da tafiye-tafiyen aiki da shugaban kasar yake.

Tafiyar da shugaba Buhari ya yi ta baya bayanan ita ce zuwa taron kolin kasar Rasha da kasashen Afirka, sai kuma babban taron da sarkin Saudiyya ya gudanar na kasashe masu rijiyoyin Mai da kuma masu zuba hannun jari. Haka kuma, Mallam Garba Shehu ya bayyana cewa shugaban Najeriya zai kai wata ziyara ta kashin kansa Birtaniya.

Saurari hirar da Yusuf Aliyu Harande ya yi da Mallam Garba Shehu.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Cece Kuce Game Da Yawan Yawon Shugaba Buhari Na Duniya