Masana a Najeriya na ci gaba da mayar da martini game da halin da tattalin
arzikin kasar ke ciki, yayin da ake muharawa kan sabon kudin takardar ECO.
Abin ke nan da masana ke cewa kasuwannin hannun jarin kana fama da masassarar rashin sanin makomar kasa game da batun shiga wannan tsarin na bai daya a Yammacin Afirka.
Matakin da Faransa ta dauka na jagorantar wasu kasashen Yammacin
Afirka na amincewa da takardar bai dayan ta ECO, ya sa kokwanto a
tsakanin masana tattalin arzikin Najeriya.
Hakan ya sa wasu ke ganin, ya kamata gwamnatin kasar ta sake tunani, kan shirin, ganin yadda Faransa take juya akalar kasashen Faransa da ta rena.
Dr. Dauda Mohammad Kontagora masanin tattalin arziki a Najeriya, ya ce tuni dai wannan rashin tabbas ya janyo fargaba ga masu saka jari a
kasuwannin hannayen jarin kasar.
Rahotanni sun yi nuni da cewa, hamshakin dan kasuwannan dan Najeriya Aliko Dangote, shi ma ya ce zai karkatar da wasu hannayen jarinsa zuwa kasar Amurka, ganin yadda takardar kudin Naira, ko sauyawa zuwa ECO ba shi da tabbas.
Sai dai a yayin da masanan ke fargaba, a cewar shugaban bankin raya
Afirka Dr. Akinwumi Adesina, wannan ba a bin fargaba ba ne.
Yanzu dai 'yan Najeriya da sauran kasashen na Yammacin Afirka sun zuro
ido domin ganin ko Najeriya za ta shiga tsarin ko kuma a’a.
Ga rahoto cikin sauti daga Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5