A daidai lokacin da ake ci gaba da fama da hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, kwamitin tsare-tsaren manufofin kudi na babban bankin kasar wato MPC na CBN ya kara yawan kudin ruwa da ake kakabawa a kan rance a bankunan kasar da maki 200 wanda ya tashi daga kaso 22 da digo 75 zuwa kaso 24 da digo 75 lamarin da masana tattalin arziki ke cewa za a iya amincewa da matakin idan har na gajeren zango ne.
Gwamnan babban bankin Najeriya wato CBN, Olayemi Cardoso, ya yi bayani a kan matakai 5 da kwamitin manufofin kudi na bankin suka cimma a taronsu na wannan karon wadanda suka hada da kara yawan kudin ruwa da 200 zuwa 24.75 daga 22.75%. 2, sai kuma daidaita hanyar asymmetric na MPR akan maki 100 zuwa 300, da riƙe adadin ajiyar kuɗi na bankunan kasuwanci kan kaso 45 cikin 100 da dai sauransu.
Wannan matakin dai na nufin cewa sabon kudin ruwan ya tashi ne daga kaso 22.75 bisa dari da kwamitin MPC ya sanar kusan wata daya da ya gabata da kuma karin shi ne karo na biyu da kwamitin karkashin jagorancin gwamna Olayemi Cardoso ke dauka.
Daraktan sashen manufofin kudin bankin CBN kuma sakataren kwamitin, Dakta Muhammad Musa Tumala, ya yi karin bayani a kan matakan da bankin CBN ya dauka yana mai cewa kara kudin ruwa wani mataki ne na gajeren lokaci da zarar abubuwa sun daidaita za’a koma yadda ake a da.
A wani bangare kuwa masanin tattalin arziki, Mallam Kasim Garba Kurfi ya bayyana cewa matakin bankin CBN bai zo da mamaki ba saboda halin da Najeriya ta sami kan ta.
Matakin na MPC na ranar Talata ya zo ne a daidai lokacin da hukumomin Najeriya suka yi ta daukar tsauraran matakai kan dandalin musayar kudadde wato cryptocurrency na kamfanin Binance.
Idan ana iya tunawa a wani mataki na tsaida tashin farashin dala, an tsare wasu shugabannin kamfanin na Binance a Najeriya matakin da ya daga darajar naira. Saidai a ranar Litinin ne rahotanni suka yi nuni da cewa daya daga cikin jami’an kamfanin Binance ya tsere daga inda yake tsare.
A bisa alkaluman kididdiga daga shafin yanar gizon bankin CBN, ana sayen kowace dala a kan naira dubu 1 da 415.134 kuma daga watan Mayun shekarar 2023 zuwa Disamba an canja kowace dala a kasuwannin bayan fage tsakanin naira 640 zuwa 990.
Bankin CBN dai ya tsaida ranar 20 zuwa 21 ga watan Mayun shekarar nan a matsayin ranar taron kwamitin MPC na gaba.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5