Canada Za Ta Tallafawa Wadanda Rikicin Boko Haram Ya Shafa A Najeriya

Firai Ministan Canada Justin Trudeau.

Kasar Canada ta ce za ta ba da tallafin kudi dalar Amurka miliyar 27, domin agazawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa a Najeriya.

Ofishin jakadancin kasar Canada a Najeriya, ya ba da sanarwar cewa Gwamnatin kasar za ta ware dala Miliyan 27 a matsayin wani sabon tallafin da ta ke baiwa Najeriyar, don taimakawa al’ummar da rikicin boko haram ya shafa a yankin arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar ta bayyana cewa ‘ kimanin mutane miliyan 4.4 ne za su bukaci taimako na abinci a yanayin da kasar take ciki a wannan shekara ta 2021.

Ta kara da cewa akalla mutane dubu 775 ke fuskantar matsalar karancin abinci sakamokon hare-haren da 'yan ta'adda ke kai musu, kazalika da barazanar yankewar kai abinci da sauran kayayyakin agaji a yankunan da ke bukatar agajin gaggawa sakamokon yawaitar hare-haren.

Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji

‘’Kudin zai taimaka wajen samar da kayan abinci masu gina jiki da magunguna da kuma tsaftatacen ruwa sha da dai sauransu,’’ in ji sanarwar ta ofishin jakadancin Canada.

Fiye da shekaru goma ke nan da ake fama da tashe-tashen hankula a yankin na Arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya sa yankin ya ke bukatar agaji da jinkai mafi girma a duniya.

Makamai Masu Linzami Sun Fada Cikin Gidaje Sakamakon Fafatawa da Boko Haram

Hare-haren yan kungiyar Boko Haram yayi sanadiyyar dubban mutane, kana kuma ya daidaita mutane dama da aka raba da matsuguninsu.

A halin da ake ciki yanzu mutane sama da miliyan takwas ke bukatar taimako na jinkai a wannan shekara ta 2021.