Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN, ta ba da gudumuwar kayayyakin abinci da kuma kekunan dinki ga 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, inda suke samun mafaka a sansanoni 'yan gudun hijira da ke Cocin EYN a garin Maiduguri.
Kungiyar ta ba da gudumuwar buhunhunan shinkafa guda 500 da kekunan dinki guda 50 da kuma tsabar kudi Naira miliyan7 don taimakawa 'yan gudun hijirar da adadinsu ya kai kusan mutum 3000.
Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya, Rev. Dr. Samson Ayokunle, ya mika wannan gudumuwa yayin da ya ziyarci sansanin.
Sananna ya yi kira da shugabanin al’umma da wakilan gwamanti da su kasance masu gaskiya kuma masu kishin kasa fiye da abin da za’a samu don su tona aisirin wadannan tsiraru da ke cikin al’umma don sauran mutane su ci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali.
Shi ma shugaban cocin EYN da ke unguwar Wulari a Maiduguri, Rev. Bitrus Mahmuda, ya ce mutane da dama suna cikin damuwa saboda wasu an kashe mazajansu wasu kuma ‘ya ‘yan su, sannan ya yi kira da gwamnati da ta kai masu dauki
Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Biu daga Maiduguri:
Your browser doesn’t support HTML5