CAN: Reshen Matasa Yayi Kira A Zauna Lafiya

Injiniya Daniel Inji, shugaban kungiyar hadin kan kirista ta Najeriya, reshen matasa

Kungiyar hadin kan Kirista a Najeriya, reshen matasa yayi Allah wadai da matsayin wadanda ke neman raba kawunan al’umma a kasar.

Shugaban reshen matasa na kungiyar hadin kan kiristocin Injiniya Daniel Kazai yace lokaci ya yi da matasa zasu yi aiki tare domin kare Najeriya, da ganin ci gaban kasancewarta tsintsiya madaurinki daya kamar yadda aka hadeta a shekarar dubu tara da goma sha hudu.

Injiniya Kazai yace abinda ya tsonewa ‘yan Najeriya baki daya ido, da ya kamata su hada hannu a kai shine ganin sun kori wadanda ya kira “barayin Najeriya” da mutanen dake kawo tada zaune tsaye a kasar domin a sami zaman lafiya.

Yace baiga dalilin da za a tilastawa wani yin addinin da ransa bai dauka ba, ko ribar da wani bangare zai ci da neman a raba kasar ba, kasancewa babu wani yanki a Najeriya da zai iya rayuwa ba tare da dayan ba.

Kungiyar tayi wannan kiran ne bayan ganawar mukaddashin shugaban kasar Najeriya Yemi Osibanjo da sarakunan gargajiya da kuma shugabannin addinai domin neman gano yadda za a warware wannan zaren.

A nashi tsokacin, Yariman Mori, Isa Tafida Mafindi, yace daukar wannan matakin zai yi fa’ida, domin bisa ga cewarshi, ko’ina ka shiga a Najeriya kana iya yin sana’ar da ka ga dama, kuma idan kaje manyan garuwa kamar Lagos ba zaka iya banbance gidaje bisa ga kabilar masu gidajen ba.

Shima da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan batu, tsohon gwamnan jihar kaduna Saneta Ahmed Makarfi yace ya kamata a ci gaba da tattaunawa har sai an sami masalaha.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Nasiru Adamu Elhikaya ya hada mana.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasan CAN sun nemi hadin kan kasa-2'59