Shugaban kwamitin marayu na Abuja, Alhaji Saidu Musa Yelwa, a jawabinsa a lokacin raba kayan abinci da tufafe ga marayu, zaurawa da miskinai, a goman Azumin karshe na watan Ramadan, ya ce a fadar Gwamnatin tarayya aka a Abuja, bai kamata ba ace marayu a Abuja suna galabaita ba.
Alhaji Musa Yelwa, wanda ya doshi shekaru tamanin a duniya yayi fatar cewa ko bayan rayuwarsa wani kyakkyawan aiki zai tore yana mai cewa yaran da suke gararamba ba karaku a kauyuka abin sai wanda ya gani.
Ya kara da cewa wadannan yara idan ba a kula dasu ba aka sake suka zama ‘yan ta’adda to tabbashi hakika zasu sa Abuja ya gagari jama’a zama.
Wadanda suka amfana da tallafin sun kai mutane dari shida inda aka ga taron yara da mata da kuma zaurawa a Masallaci jum’a na Umar Bin Kattab, a Utako, a Abuja, suna karban abinda ya sauwaka na wannan tallafin.
Shugaban zaurawan Hadiza Muhammad, tace kwamitin na taimakawa gaya kama daga koyarda da sana’oi, abinci, sitiru da kuma kudaden jari na fara sana'a.
Sarkin Hausawan Yanyan, Malam Musa Dala, yace a matsayinsu na shuwagabanin al’uma suna dorawa shuwagabanin a tsakanin su haraji na abinda kowa zai kawo kuma suna bin masu abun hannu domin neman taimako wanda irin wadannan taimakon ne ya kawo abinda aka tara zuwa yau.
Facebook Forum