Hukumar dake kula da wasan kwallon kafar Afrika CAF, ta ba da umurnin kungiyar kwallon kafa ta Esperance Tunisiya da ta dawo da Kofi da kuma lambobin yabo Medal, da ta samu a wasan karshe na zakarun kungiyoyin Afrika.
Hukumar ta kuma umurci da a sake buga wasan da Wydad Casablanca ta Morocco, zubi na biyu da aka yi watsi da shi ana tsakar fafatawa.
Hukuncin dai ya jefa wasan kwallon kafa a nahiyar ta Afirka cikin rudani, inda saura 'yan makonni suka rage a fara gasar cin kofin nahiyar Afrika da kasar Masar za ta karbi bakonci a wannan wata ta Yuni da muke ciki.
Tun da farko Alkalin wasan ya ba da nasara ga kungiyar kwallon kafa ta Esperance, inda ita kuma Wydad Casablanca ta Morocco ta yi watsi da sakamakon, saboda rashin na’urar da ke taimaka wa alkalin wasa wato VAR, da zai tantance wata kwallo da Wydad din ta farke.
Alkalin wasan ya soke lokacin Esperance ne da ke kan gaba da ci 1-0 a wasan na biyu, jimilla 2-1 yayin da wasan ya tsaya, bayan jinkiri na mintuna 90, alkalin wasan ya baiwa kungiyar da ke wasa a gida, wato Esperance nasara.
Babban jami’i a ofishin shugaban CAF Hedi Hamel ya ce baya ga rashin cika ka’idoji na wasa, akwai matsala ta tsaro yayin wasan na biyu, lamarin da ya hana a karasa wasan, saboda haka za a sake wasan bayan gasar cin kofin nahiyar Afirka da za fara daga ranar 21 ga watan Yunin nan zuwa 19 ga watan Yuli.