Cikin wata sanarwar da ta wallafa a shafinta na internet, ISWAP tace mayakanta sun yiwa sojojin Najeriya kwantan bauna akan hanyar Maiduguri zuwa Damboa, inda suka kashe sojoji arba'in tare da kwace motocin sojin guda biyar.
ISWAP tace ta kuma kai karin hare-hare a Khaddamari da Gubio, inda nan ma tace ta kashe wasu sojojin.
To amma cikin martanin da ta mayar, Hedikwatar tsaron Najeriya tace dakarunta sun yi arangama da wasu 'yan ta'adda a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa inda su ka kashe yan ta'adda goma sha bakwai.
Sojojin suka ce sun kuma kwato kayan yaki daga 'yan ta'addar, yayin da wasu da dama kuma suka tsere da raunuka.
Wani mai bincike kan kungiyar 'yan ta'addan, Dr. Kabiru Adamu ya ce lalle kam an fafata tsakanin bangarorin biyu, amma zai yi wuya a hakikance ainihin gaskiyar abin da ya faru.
Sanannen abu ne cewa kowane bangare ya kwarzanta irin nasarar da ya samu sannan ya boye irin barnar da aka yi masa.
Shi ma wing commander Musa Isa Salman da ke zama tsohon hafsa a rundunar sojojin kasar, ya ce koma mene ne irin hare-haren da 'yan ta'addan ke ta kaiwa ba kakkautawa, na nuna cewa akwai bukatar sake duba yadda dakarun ke fuskantar wannan yaki.
A cikin kwanakin nan ana yawan musayar wuta a tsakanin sojojin da 'yan ta'addar wanda ke haifar da mace-macen mutane da dama.