BURUNDI: Yau Za'a Jefa Kuri'ar Raba Gaddama Akan Karawa Shugaban Kasa Wa'adin Mulki

Pierre Nkurunziza shugaban Burundi dake neman tsawaita wa'adin mulkinsa

Yau Alhamis ne 'yan Burundi zasu jefa kuri'ar tsawaita wa'adin mulkin shugabansu ko kuma su yi watsi da bukatarsa kodayake wasu 'yan kasar na ganin kome ya faru shugaban zai yi abun da ya ga dama ne

Yau Alhamis din nan cikin yarda Allah ‘yan kasar Burundi zasu jefa kuri’a jin ra’ayi ko raba gardama akan yiwa tsarin mulkin kasar kwaskwarima.

Galibi ‘yan kasar suna dari darin fadin ra’ayin su akan wannan zabe domin tsoron kada gwamnati ta musguna musu. To amma daga cikin mutane kalilan da suka yi magana shine wani taila mai suna Victor Kabera Taila, wanda yace shi abinda yake so shine tsaron lafiyar sa da wurin da zaiyi aiki.

Yace kuri’ar bata da wani muhimmanci a wurinsa. Domin koda za’a yi shekaru biyu zuwa uku nan gaba, ‘yan siyasa zasu yi abinda suke so. Yace mutane abinda ya dame su shine matakan tsaro.

Kwaskwarimar da za’a yiwa kundin tsarin mulkin kasar da ake cacar baki akansa zai fadada wa’adin mulkin shugaba Pierre Nkurunziza daga shekaru biyar zuwa bakwai. Tun shekara ta dubu biyu da biyar shugaba Nkurunziza yake jan ragamar mulkin kasar. Shawarar daya yanke na neman wa’adi na uku a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar ta haddasa tarzoma da hargitsi data tilasta ‘yan kasar dubu dari hudu arcewa daga kasar.

Jam’iyar CNDD FDD wadda take jan ragamar mulkin kasar tace canje canje zasu kawo kwanciyar hankalin siyasa a kasar. To amma masu cacakar wannan mataki, sun ce babu abinda canje canjen zasu haifar, illa karfafa ikon shugaba Nkurunziza.