Karo na farko, Daruruwan mutane suka bi titi a babban birnin Burundi wato Bujumbura domin zanga-zangar nuna kyamar su tun bayan juyin mulkin da baiyi nasara ba a kasar cikin satin da ya gabata.
Wakilin wannan gidan Radiyon Gabe Joselow ya ruwaito cewa sojojin kasar sun dauki matakan tsaro masu tsauri domin hana zanga-zangar nuna kyamar gwamnati.
Masu zanga-zangar dai sun taru a inda suka saba taruwa cikin birnin suna cewa yunkurin sake tsayawa takara da shugaba Pierre Nkurunziza ke yi ya sabawa dokar kasa.
A lokuttan baya dai da masu zanga-zangar sunyi ta jifar yan sanda daga baya kana sun sa shingaye sun tsare hanya, yayin da yan sanda suka mayar da martini ta harba barkonon tsohuwa da harsashi mai iya kashe mutum.
Sai dai anga sojoji sun tsaya tsakanin masu zanga-zanga da yan sanda domin hana barkewar tarzoma, tsakanin bangarorin biyu.