Burundi: An Fara Shari'ar Sojoji da 'Yansanda da Suka Yi Yunkurin Juyin Mulki Watan Mayu

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza.

A watan Mayun wannan shekarar ne wasu sojoji da 'yansanda suka yi yunkurin kawar da shugaban kasar wanda ya shirya ta zarce a karo na uku abun da kundun tsarin mulkin Burundi bai bashi ba.

A Burundi an fara shari'ar wasu manyan hafsoshin sojin kasar dana 'Yansanda su fiyeda 28 kan zargin suna da hanu a wani yunkurin juyin mulki gwamnatin shugaba Pierre Nkurunziza.

Ranar Jumma'a data shige ne wadanda ake zargin su 28 ciki harda tsohon ministan tsaron kasar Cyrille Ndayirukiye da wasu masu mukaman janar janar su biyar ne suka bayana gaban wata kotu a garin Gitega dake tsakiyar kasar.

Masu gabatar da kara sun ce ana zargin mutanan ne da yunkurin hambarar da gwanatin kasar cikin watan Mayu, da kuma kashe sojoji da tada tarzoma.

Amma lauyoyi da suke kare wadanda ake tuhuman, suka ce basu sami cikakken dama ganin file-file na wadanda suke baiwa kariya ba. Kuma sun yi zargin cewa ana muzgunawa wadanda suke karewan a fursina, kuma an tsare su a wurare da sam basu dace ba.

Tun cikin watan Afrilu ne dai Burundi take fuskantar tashe tashen hankula bayan da shugaba Pierre Nkurunziza, ya ayyana zai yi tazarce.