Yau Juma’a ne Firam Ministan Burtaniya, Theresa May, ta ajiye mukaminta na shugabancin Jam’iyyarta, ta masu ra’ayin ‘yan mazan jiya – Conservative Party, kuma ana san ran a sati mai zuwa za’a gudanar da zaben wanda zai gaje ta.
May zata ci gaba da rike wannan mukanin har zuwa lokacin da za’a zabi wanda zai gaje ta.
Sai dai ana sa ran za’a tsayar da sabon shugaba zuwa karshen watan Yuli.
Amma kafun nan, zata ajiye iko akan duk wani batu da ya shafi ficewar Burtaniya daga kungiyar tarayyar turai, wanda aka diba ma lokaci har zuwa 31 na watan Oktaba na bana.
Firai ministan da zai maye gurbin May na da kasa da watannin biyar ya yanke shawarar ko zai ci gaba da fafutukar aiwatar da shirin May, na jinkirta ficewa daga kungiyar tarayyar turai, ko kuma su bar EU ba tare da wata yarjejeniya ba gaba daya.