Sai dai a yayin da gwamnatin Faransa ke cewa ba ta fahimta abin da hukumomin Burkina ke nufi da wannan mataki ba, masana sha’anin tsaro na fassara abin a matsayin alamomin gaskiya game da zargin kamfanin Wagner da girke sojojinsa a kasar ta Burkina Faso.
A shekarar 2015 ne Burkina Faso ta amincewa Faransa ta kafa sansani mai dakaru 400 a karkashin wata yarjejeniyar da sai a watan janerun 2018 aka soma aiwatar da ita da nufin yaki da ‘yan ta’adda.
Yarjejeniyar ta bada dama ga kowane daga cikin bangarorin ya canza ra’ayi idan bukatar haka ta taso, dalili kenan gwamnatin Burkina Faso ta dibarwa Faransa wata guda ta kwashe sojojinta saboda a cewarta an zo karshe.
Matakin da a yanzu haka ya fara daukan hankulan masu fashin baki akan al’amuran yau da kullum kamar su shugaban gamayyar kungiyoyin Resaeu Esperance Bachar Mahaman.
A watan da ya gabata, shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo ya yi hasashen cewa kamfanin Wagner na sojojin hayar Russia ya shigar da askarawansa a kasar Burkina Faso, abin da ya haifar da tayar da jijiyoyin wuya a wancan lokaci, amma a cewar masanin sha’anin tsaro Abass Moumouni sabon matsayin gwamnatin ta Kanal Ibrahim Traore alama ce dake nunin biri ya yi kama da mutum.
Sace matan nan ‘yan Burkina Faso sama da 50 da rahotanni suka ayyana a farkon makon jiya, abu ne da gwamnatin kasar ke zargin shiri ne da aka kitsa takanas daga ketare a cewar ministan sadarwa Rimtalba Jean Emmanuel Ouedraogo, saboda haka masana ke alakanta matakin korar Sojan na Faransa da wannan al’amari.
Shugaba Macron dake bayani wa kafafen labarai a washegarin bayyanar labarin daukan wannan mataki ya ayyana cewa bai fahimci abin da gwamnatin Burkina Faso ke nufi ba da bukatar ficewar dakarun Faransa daga kasar saboda haka ya ce ya yi fatan a yi masa Karin haske akan wannan labari.
Saurari rahotan Sule Muminu Barma:
Your browser doesn’t support HTML5