Amurka ta ce babu abin da ta maida hankali akai kamar ganin Najeriya ta gudanar da zaben 2019 tare da mika mulki cikin kwanciyar hankali.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, ya fadi hakan ne yayin wani jawabin da ya yi a New York a matakin fara shirye-shiryen ziyarasa zuwa Afrika, wanda jaridun Najeriya suka ruwaito daga kamfanin dillancin labaran Najeriya na NAN.
Ziyarar ta sa zai fara ta ne daga ranar 6 zuwa 13 ga watan nan na Maris.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana cewa cikin shekaru 20 da suka gabata, kasashen da ke da zababbun gwamnatoci ba su da yawa a Afirka, tana mai cewa ba su wuce uku ba zuwa hudu ba.
“Wannan yanki (Najeriya) yanki ne da muka maida hankali akai kan yadda za a mika mulki cikin lumana bisa tubar dimokradiyya, amma abu mafi muhimmanci shi ne yadda za a tursasa gwamnatoci su kasance suna mika wuya ga bukatun mutanensu.” Inji Tillerson.
“Idan muka kalli zabuka 20 da za a yi, misali Najeriya, ko da yake, ba a wannan shekara ba ne…. wannan abu ne mai muhimmanci, saboda kasar za ta zama kasa mafi yawan al’uma ta uku a Duniya nan da 2050.” Tillerson ya kara da cewa.
Najeriya dai na da yawan kabilu sama da 200, hakan ya sa wasu masu lura da al’amura suke ganin ya sa kasar ke fama da matsololin kabilanci da kuma tsaro.
A cewar Tillerson Najeriya “na da batutuwan siyasa masu sarkakiya da na kabilanci da kuma tsaro.” Kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.
Wannan ce ziyayar farko da Sakataren harkokin wajen Amurka Tillerson zai kai nahiyar.
Kuma ziyarar na zuwa ne kasa da wata biyu bayan da shugaban Amurka ya kwatanta nahiyar ta Afirka a matsayin kasakantaccen wuri.