Burina Shine Naga Masa'antar Kannywood Ta Cigaba: Abdulaziz Abba Abubakar

Abdulaziz Abba Abubakar – Editan fina-finai wanda ya shafe shekaru kimanin 15 yana masana’antar Kannywood, ya ce babban matsalar da ke ciwa harka editin tuwo a kwarya ita ce rashin cigaba a labari, ma’ana mafi yawan lokuta babu daidaito wajen kula da sutura ko yanayi na daukar hoto a fina-finai.

Ya ce da dama a cikin fim akan sami a fitowar farko a nuna mace da kalar kayan jikinta, amma daga shiga daki zuwa fitowa zaka ga suturar ta canza, yadda har ta kan kai ga mai kalo ya lura da wani banbamci, a cewarsa yana daga cikin abinda suke maida hankali a kansa a yanzu.

Ya kara da cewa a mafi yawan lokuta a da, ba’a fita da edita sabanin yadda ake yi a yanzu, inda mafi yawan masu shirya fina-finai ana fita da su domin kauracewa ire-iren kura-kuran editin.

Ya kara da cewa a da rashin fita da su kan haifar da yawan samun rashin tashin sauti, canji ga yanayin sutura da sauransu.

Abdulaziz ya ce har yanzu gwamnati da masu hannu da shuni sun ki su zuba hannun jari a masana'antar, alhali a hannu guda kuwa suna yawaita korafin cewar 'yan fim na bata al’ada, bayan sun ki shigowa harkar fina finai domin tabbatar da an kawo gyaran da ake bukata.

Your browser doesn’t support HTML5

Burina Naga Masa'antar Kannywood Taci Gaba: Abdulaziz Abba Abubakar 05'09"