Bukukuwan Kirsimeti: Tinubu Ya Amince Da Sufuri Kyauta A Fadin Najeriya

Sabon Layin Jirgin Kasa Na Abuja

Sabon Layin Jirgin Kasa Na Abuja

gwamnatin tarayya za ta kaddamar da tsarin sufurin jiragen kasa kyauta daga ranar 20 ga watan Disamban da muke ciki zuwa 5 ga watan Janairun 2025.

Shugaba Bola Tinubu ya amince da sufuri kyauta a fadin Najeriya gabanin bukukuwan kirsimeti.

Ministan yada labarai da wayar da kan al'umma, Muhammad Idris, ne ya sanar da hakan yayin ganawarsa da manema labaran fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya karkashin jagorancin shugaban kasar a yau Litinin.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya za ta kaddamar da tsarin sufurin jiragen kasa kyauta daga ranar 20 ga watan Disamban da muke ciki zuwa 5 ga watan Janairun 2025.

Ministan yada labaran ya tabbatar da cewa wannan taron majalisar zartarwar shine na karshe a bana, kuma majalisar za ta tafi hutu tun daga 18 ga watan Disamban da muke ciki har zuwa 6 ga Janairun 2025.