Mr Joseph, ya bayyana cewa su ma a kafar Talabijin suka ga zaman, ya kara da cewa da ace majalisar Dattawan ta gayyace su, da sun halarci zaman domin bada bayani dalla dalla akan motar nan kirar Range Rover, mai sulke da jami’an suka kama a jihar Lagos, cikin watan Janairu, wadda aka yi zargin shugaban majalisa Bukola Saraki ne ya shigar da ita kasar ba tare da biya mata haraji ta hanyar data dace ba.
Harajin wannan mota ya kamata ya kasance Naira Miliyan Saba’in da Hudu, jami’in ya bayyana cewa duk wani jawabi da majalisar ke bukata kan wannan mota, a shirye suke domin bada bahasi.
Da suke zama, kwamitin majalisar dattawan, shugaban majalisar Bukola Saraki, ya bayyana kuma ya musanta sayen wannan mota mai sulke, ya kara da cewa yawancin motocin wannan majalisa, bazaka taba sanin anyi odarsu ba sai dai kawai ka gansu, ya kuma nuna cewa wannan mota mallakar majalisar dattawa ce, kuma kowane shugaban majalisar na iya aiki da ita.
Bukola Saraki, ya kara da cewa ya bayyana gaban kwamitin ne domin mutumta darajar majalisa da ya dace su kare, domin ita ta banbanta mulkin soji da na farar hula. Ana sa ran Talatar makon gobe shugaban hukumar Kwastam ko wani jami’i zai bayyana a gaban kwamitin majalisar domin Karin bayani kan wannan mota.
Jama’a da dama na ci gaba da muhawara kan matsin lamba da majalisar ta yi wa shugaban hukumar kwastam na kasa kan sai ya sa kayan sarki da kuma kira yayi murabus yasa shugaban majalisar dattawan ya bayyana gaban kwamitin domin ya nuna shi mai mutunta doka ne.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5