Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Mataimakin Shugaban Makarantar Sakandire Bisa Zargin Lalata Da Dalibai Mata 6 A Jihar Neja


Hukumar kare hakkin yara a jihar Neja, na gudanar da bincike akan mataimakin shugaban makarantar sakandiren gwamnati ta gidan Kwano, dake Tunga, a Minna, mai suna Mohammed M. Kweji, bisa zargin yin lalata da wasu ‘yan matan sakandiren guda shidda.

Daya daga cikin daliban da aka sakaya sunanta ‘yar aji uku mai shekaru Goma sha Shidda da haihuwa ta bayyana cewa a yanzu haka tana dauke da juna biyu a sakamakon kwana da yayi da ita a ofishinsa.

Yayin da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari ya gana da wanda ake zargin, ya bayyana masa cewa ya aikata wannan laifi amma ba da son ransa ba, domin a cewar sa, dalibar tamkar diyarsa ce, kuma ta same shi a ofishinsa ne yayin da daliban ke komawa hutu, ya kuma kara da cewa sauran daliban guda shidda ma duk lamarin dai ba’a cewa komai.

A yanzu haka hukumar kare hakkin yara ta jihar Neja, ta ce zata bi lamarin sau da kafa kamar yadda shugabar hukumar Barrister Maryam Kolo, ta yi Karin bayanin cewar tunda ya amsa laifinsa kuma an sami wasu ‘yan matan har guda shidda, ya zama wajibi hukumar ta ba jami’an tsaro alhakin gudanar da binciken lamarin.

Kwamishiniyar ma’aikatar ilimin jihar Hajiya Fatima Madugu, ta bayyana cewa tana sane da lamarin amma sai ta kammala gudanar da nata binciken zuwa karshen wannan mako zata yi wa manema labarai jawabi.

Domin Karin bayani, saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG