Bukola Saraki Ya Je Jaje Jihar Filato

Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki

Shugaban Majalisar dattijai Bukola Saraki ya jagorancin tawagar majalisar zuwa gaisuwar jajae ga gwamnatin jihar Plato biyo bayan hare haren da aka kashe sama da mutane dari biyu

Da yake jawabi a wajen wannan ziyara, shugaban majalisar ya bayyana takaicin aukuwar wannan lamarin, da yace asara ce da ta shafi kasa baki daya ba jihar Plato kadai ba. ya kuma mika gaisuwar ta'aziya a madadin majalisa baki daya.

Saraki ya bayyana cewa, " ba za a iya bayyana irin bakin cikin da dangin wadanda aka kashe suke ciki ba a halin yanzu"

Tun farko, Shugaban majalisar Bukola Saraki ya buga a shafinsa na twitter cewa tawagar zata kai ziyara jihar Plato ne domin ganin da ido da kuma jajantawa al'ummar jihar.

Kafin ziyarar tasa, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kuma mataimakinsa, Yemi Osinbajo sun kai irin wannan ziyarar cikin kwanaki biyu da suka shige inda gwamnatin tarayya ta kara jadada niyarta ta shawo kan irin wadannan rikice rikice da ake dangantawa da addini da kuma kabilanci.

Tun farko, Shugaban majalisar dattijan ya shawarci gwamnatin tarayya ta dauki kwararan matakan tsaro a jihar da ake fama da yawan hare hare dake janyo asarar rayuka da kaddarori.

https://twitter.com/SPNigeria/status/1011009297843720192