Wata sanarwa da mai baiwa shugaba Buhari shawara kan harkar yada labarai, Femi Adesina ya fitar, ta nuna cewa Buhari zai koma gida ne bayan da likitocinsa suka amince da hakan.
Tun a ranar 19 ga watan Janairu Buhari ya tafi London inda ya je hutun kwanaki goma tare da ganin likita bayan wata wasika da ya aikewa majalisar dokokin kasar.
Sannan ya sake tsawaita hutun nasa bayan da likitoci suka ba shi shawara ya tsaya ya ga sakamakon wasu gwaje-gwaje da aka yi masa kamar yadda Fadar shugaban kasar ta bayyana.
Zaman jinyar na shugaban Najeriya a London ta haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan kasar musamman kan halin da yake ciki.
Tun dai da Buhari ya tafi ba a ji muryarsa ba sai a lokacin wani taron addu'a da aka shirya masa a jihar Kano inda ya yi godiya ga masu masa addu'ar a wata tattaunawar waya tarho da suka yi da gwamna Abdullahi Ganduje.
Ko da yake gabanin hakan an ta ganin hutunansa da wasu a suka rika kai mai ziyara a lokacin yana jinyar.
Tun kafin ya kama hanyarsa ta zuwa London, shugaba Buhari ya riga ya baiwa mataimakinsa Yemi Osinbanjo cikakken ikon zama mukaddashin shugaban kasa, lamarin da ya sassauta muhawara kan makomar mukamin.
Domin jin karin bayani saurari hirar Mahmud Lalo, a Fadar Shugaban kasar, Umar Faruk Musa wanda ya ga sanarwar da femi Adesina ya fitar.
Your browser doesn’t support HTML5