Buhari Zai Karrama Limamin Da Ya Ba Wa Kiristoci Mafaka a Jihar Filato

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari zai karrama Imam Abdullahi Abubakar, wanda da ya bai wa kiristoci fiye 300 mafaka a masallaci da gidansa a lokacin da rikici ya barke a Barikin Ladi na baya-bayannan a Jihar Filato.

Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ne ya bayyana hakan a yayin wani taron sulhun da hukumar sasanta tsakanin al'ummar Jihar ta shirya. Gwamnan ya jinjinawa Imam Abdullahi Abubakar inda ya ce, ya yi wani abun da ba kasafai ake samu ba musamman a lokacin tashin-hankali.

"Allah kadai zai iya saka maka," inji Gwamnan domin alherin da yayi, Allah ne kadai zai iya biyansa.

Gwamna Lalong ya yi alkawalin tallafawa 'yan gudun hijira fiye dubu talatin da bakwai a sassa dabam-dabam na jihar. Ya kuma ce gwamnati za ta ci gaba da gina tubalin zaman lafiya.

"Ba zamu gaza ba wajen sadaukar da kai domin shawo kan matsalar tsaro duk da kulle-kullen da miyagu ke yi don mayar da hannun agogo baya kan zaman lafiyar da muka cimma," in ji Lalong.

Mukaddashin jakadan Amurka a Najeriya, David Young, wanda ke ziyara a jihohin da ake fama da yawan zubda jini, shi ma ya halarci taron inda ya tunatar da al'umma kan su dukufa wajen ayyukan da za su kawo hadin kan jama'a da ceton rayuka maimakon zubda jini.

"Al'umma daga bangarori dabam-dabam za su iya samun adalci ba tare da sun dauka matakan da za su kai su ga kisa ba," inji Young.

Saurari cikakken rohoton Zainab Babaji

Your browser doesn’t support HTML5

Buhari Zai Karrama Limamin Da Ya Ba Wa Kiristoci Mafaka a Jihar Filato - 2' 19"