Buhari yace ba zai karya darajar Naira ba amma Falana ya garzaya kotu

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Kodayake shugaban kasa yace ba zai karya darajar nera ba shahararren lauya Femi Falana ya garzaya kotu domin ta hana babban kankin Najeriya kwatanta nera da dalar Amurka

Shahararren lauyan Femi Falana mai fafutikar kare hakin bil Adama ya garzaya kotu yana neman ta hana babban bankin Najeriya da auna mizanin tattalin arzikin kasar da dalar Amurka.

A cewarsa cigaba da auna takardar kudin nera da kudin dalar Amurka ba wani abu yake haifarwa kasar ba sai dai koma baya ga tattalin arziki da kuma mayar da kasar tamkar 'yar amshin shata.

To amma a cewa masana tattalin arziki sun ce matasyin na Femi Falana ba hujja ba ne ta fuskar tattalin arziki da kuma hada hadar kudi a duniya

Malam Kasumu Garba Kurfi yace komi ana duba daidai karfin tattalin arzikin kasa ne. Yace a kasashen yammacin Afirka banda saifa da aka tilastawa ksashen renon Faransa suna anfani da ita koina mutum ya je batun nera ake yi saboda karfin tattalin arzikin kasar. Karfin tattalin arzikin kasar ya sa dole kowace kasa a yammacin Afirka ta yi da kasar.

Haka yake a duk duniya ko mutum ya yi haraka da dala ko ya bari amma kuma dole ya dawo kanta. Yau idan Amurka tace ba zata sayi kayan China ba to ta shiga uku.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban kasa yace ba zai karya darajar nera ba amma Falana ya garzaya kotu - 3' 16"