Buhari Ya Umarci Ministocin Da Za Su Tsaya Takara Su Yi Murabus

Taron majalisar zartarwa a Najeriya (Hoto: Facebook/Fadar shugaban kasa)

Sai dai wannan umarni a cewar fadar shugaban kasar bai shafi mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osibanjo ba, saboda shi an zabe shi ne.

Rahotannin daga Najeriya na cewa, Shugaba Muhammadu Buhari, ya umarci mambobin majalisar zartarwarsa da ke da sha'awar tsayawa takara a zaben 2023 da su ajiye aikinsu.

An ba su daga nan zuwa ranar 16 ga watan Mayun 2022.

Buhari ya ba da wannan umarnin ne a zaman majalisar zartarwar da aka yi a ranar Laraba kamar yadda ministan yada labarai da ala'du, Lai Mohamed ya fadawa manema labarai bayan taron.

Sai dai wannan umarni a cewar Mohamed, bai shafi mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osibanjo ba, saboda shi an zabe shi ne.

Kadan daga cikin wadanda wannan umarni ya shafa akwai ministan sufuri Rotimi Amaechi, ministan shari'a Abubakar Malami, ministan kwadago, Chris Ngige, Ministan yankin Niger Delta, Godswill Akpabio, ministar mata Pauline Tallen da sauransu.

Wani abu da umarnin bai fayyace ba shi ne ko wadanda aka nada a wasu mukaman siyasa da ke da sha'awar takara ko su ma za su yi murabus.

Wannan umarni da fadar shugaban kasar ta fitar na zuwa ne yayin da kungiyoyin fararen hula suke nuna matsalin lamba ga gwamnati kan ta umarci masu rike da mukamai a majalisar zartarwar kasar su ajiye aikinsu muddin suna da sha'awar yin takara.

A badi ne Najeriya za ta gudanar da zabukan shugaban kasa, gwamnoni da na majalisar dokokin a matakin jihohi da tarayya.