Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da umurnin a gudanar da cikakken bincike kan wata hatsaniya da ta auku a fadarsa da ke Abuja wacce har ta kai ga aka yi harbe-harbe a ranar Alhamis.
Mai baiwa shugaba Buhari shawara kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi.
Ya kara da cewa, "Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umurni ga hukumar 'yan sanda da su yi cikakken bincike." In ji Garba Shehu yayin wata hira da ya yi da wakilin Muryar Amurka Umar Faruk tawayar taro.
"Muna so mu ba da tabbacin cewa Shugaba Muhammadu Buhari lafiya yake. kuma ba ya tattare da wata barazana ko saboda ciwo na coronavirus ko kuma wannan fitina da aka ce an yi."
Sai dai kakakin na Shugaba Buhari bai yi cikakken bayani kan abin da ya faru ba inda ya ce, "wannan bincike na 'yan sanda su za su fadawa duniya waye ya yi abu kaza ko me ya faru."
Kafafen yada labaran Najeriya da dama sun ruwaito cewa wani babban hadimin Shugaba Buhari mai suna Sabiu Tunde ne ya yi tafiya zuwa Legas amma ya ki killace kansa na tsawon kwana 14 duk da cewa an ba da umurnin yin haka a fadar ta gwamnatin kasar.
Hakan ya sa uwargidan shugaban kasar Aisha Buhari ta nemi da yi killace kansa amma lamarin ya cutura har ya kai ga samun hatsaniyar da ta janyo jami'an tsaron da ke kula da lafiyar uwargidan shugaban suka yi harbi.
Saurari cikakkiyar hirar Umar Faruk Musa da Garba Shehu:
Your browser doesn’t support HTML5