Kwarya-kwaryar kasafin kudin na Naira biliyan 242.4 ne wanda a ciki za a ware kudaden da za a yi zabe a watan Fabrairun shekarar 2019 da su.
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki ya bada bayanin kasafin kamar haka:
- Hukumar Zabe, Naira biliyan 189
- Ofishin mai bada sharwa ga shugaban kasa kan lamuran tsaro, Naira biliyan 4.2
- Hukumar tsaro ta farar hula DSS Naira biliyan 12.2
- Hukumar tsaro da ake kira Civil Defense, Naira biliyan 3.5
- Rundunar 'yan sanda Naira biliyan 30.5
Ha-kazalika, kasafin kudin zai tabo ayyuka da dama, "kamar aikin wuta na Mambila wanda ke da muhimmanci," inji Sanata Kabiru Ibrahim Gaya. Shugaba Buhari na kokarin zartar da wannan aikin a Mambilla wanda aka yi tunaninsa shekaru sama da 30 da suka wuce, amma ya gagara tabbata. Wannan aikin zai iya samar da megawatts 3050 na wuta a kasar wanda zai taimaka wajen saukaka matsalolin da karancin wuta ke haifarwa.
Sanata Gaya, ya bayyana cewa za su yi kokarin bada hadin kansu don ganin an cimma wannan buri.
"Na tabbata ko za a yi muhawara, tilas tun da sai an kai ma kwamitoci," inji Sanata Abu Ibrahim. A cewarsa, watakila ba za a samu damar yin nazarin wannan kasafi ba a yanzu, domin majalisar na shirin zuwa hutu a mako mai zuwa, kuma ba za su dawo bakin aiki ba har sai watakila a watan Oktoba.
Saurari rohoton Madina Dauda
Your browser doesn’t support HTML5