Buhari Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa

FILE - Nigerian President Muhammadu Buhari gestures as he arrives to cast a vote in Nigeria's presidential election at a polling station in Daura, Katsina State, Nigeria, Feb. 23, 2019.

An sake zaben shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a wani sabon wa’adi na tsawon shekaru hudu, duk da yunkurin da bangaren adawa suka yi, na neman a dakatar da ayyana sakamon zaben.

Shugaban hukumar zaben mai zaman kanta ta Najeriya wato (INEC), Prof. Mahmood Yakubu, ya ayyana shugaba Muhammadu Buhari, na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2019 da kuri'u 15,191,847.

Abokin hamayyarsa, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya sami kuri’u 11,262,978.

Ana sa ran shugaba Buhari zai yi wa jama’ar kasar bayanin samun nasara a hukumance, ko da yake tuni ya riga ya wallafa a shafin Twitter cewa “yana mai alfahri da nasarar da aka cimma.”

A baya, babbar jam’iyyar adawar kasar PDP, ta nemi da a dakatar da kidayar kuri’un, inda ta kafa hujjar cewa an yi arangizon kuri’u ta hanyar jirkita na’urorin tantance masu kada kuri’a.

Ko da yake har ya zuwa yanzu, jam’iyyar adawa ta PDPn, ba ta bayyana cewa ko za ta kalubalanci sakamakon zaben ba.

A baya, sai da aka dage zaben na Najeriya da tsawon mako guda, sanadiyar abin da hukumar zaben kasar ta bayyana a matsayin wasu matsaloli da aka fuskanta, wajen jigilar kayayyakin zabe.