Harkar kasuwanci tsakanin arewacin Najeriya da kudanci - kai, har ma da makwabtan kasashe - za ta bunkasa. Arewacin Najeriya musamman da ma Najeriyar baki daya za ta amfana da abubuwan arziki da ke tattare da duk wata tashar jirgin ruwa sanadiyyar gina tashar jirgin ruwan Baro.
WASHINGTON D.C. —
A wani abin tarihi ga arewacin Najeriya da ma kasar baki daya, Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da tashar jirgin ruwa ta farko a arewacin Najeriya kan kudi sama da Naira miliyan dubu 6.
Wannan wani cigaba ne musamman ma a bangaren sufuri, cinakayya da kuma tattalin arziki, wadanda ke kara dogara ga amfani da sufurin ruwa.
Wannan tashar jirgin ruwan, wadda aka kaddamar a garin Baro, tun a zamanin marigayi Shugaba Umar Musa 'Yar'aduwa aka kaddamar da aikin fara samar da wannan tashar jirgin ruwan:
Ga dai wakilinmu a Mina Musatapha Batsari da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5