A karon farko, tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya je fadar shugaban kasa ta Aso Rock da ke Abuja tun bayan da ya mika mulki a bara.
Buhari da wasu tsoffin shugabannin kasar ciki har da Goodluck Jonathan sun halarci taron majalisar kasa wanda kan gayyaci tsoffin shugabannin don tattauna matsalolin Najeriya.
Kazalika wannan shi ne taron kasa na farko da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta tun da ya karbi mulki a watan Mayun 2023.
Karo na karshe da aka yi taron shi ne wanda Buhari ya jagoranta kan matsalolin da suka taso bayan sauya fasalin kudaden Najeriya.
Taron wanda aka yi a ranar Laraba ya samu halartar tsohon shugaban mulkin soji Janar Yakubu Gowon da Janar Abdulsalami Abubakar amma ta kafar yanar gizo.
Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa taron ya duba batutuwan da suka shafi zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a kwanan nan da kuma makomar tattalin arzikin kasa.