Janar Muhammad Buhari ya fito fili ya godewa 'yan Najeriya da irin gagarumin goyon bayan da suka bashi tare da jam'iyyarsa a zabukan da suka gabata.
Janar Buhari yace ya ga goyon baya a duka jihohin da ya je. Ya yi fatan Allah ya saka masu da alheri. Ya yi farin cikin yadda jam'iyyarsa ta samu karbuwa a duk jihohin kasar.
To amma jam'iyyar PDP ta ce nasarar da Janar Buhari ya samu tare da jam'iyyarsa ba zata raunanata ba. Wai ja da bayan rago ta yi da niyyar dawowa a 2019. Jauro Hammadi Sale na PDP shi ya yi wannan harsashen. Ya ce idan mutum ya sha kaye sai ya amsa. Shugaban kasa da gwamnoni sun amsa kayen da suka sha. Yanzu sai su bari APC ta kafa gwamnati bayan watanni biyar su duba su ga irin kurakuran da suka yi kana su gyara. Yace nan da zuwa 2019 za'a sha mamakin PDP.
Akan cewa jam'iyyar zata dawo a 2019 tamkar kurarin banza ne ganin yadda 'ya'yanta ke kwararawa zuwa APC, babban mataimakin mai shari'a na PDP Bashir Maidubu yace an basu damar mulki na shekaru 16. Yanzu 'yan kasar sun nemi canji kuma sun samu. Zasu zauna su gano dalilan da suka sa suka nemi canjin su gyara. Yace gaskiya ba za'a rasa kurakuran da jam'iyyar tasu ta yi ba. Zasu duba kafin su fuskanci zaben 2019.
To saidai sabon gwamnan Bauchi yana ganin mulkin Buhari da gwamnonin APC zai yi dogon zango. Yace zasu wanzar da adalci da tabbatar da kawar da cin hanci da rashawa. Zata toshe duk hanyoyin da ake yin anfani dasu ana barna da almubzaranci da kudaden gwamnati.
Mataimakin shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya wato CAN a takaice, Rabaran Shuaibu Mpel yace kowacce jam'iyya ma ta samu nasara ya kamata a kamanta adalci. Yakamata su yiwa jama'a hidima cikin gaskiya da adalci kuma su tabbatar sun cika manufofi na zabuka da aka yi a bangarori daban daban. Wadanda kuma aka kayar su rungumi kadara cewa daga Allah abun yake. Su bi misalin abun da shugaba Jonathan ya yiwa Janar Buhari.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5