A wajen ganawar shugabannnin sun tattauna da tsara wasu manufofi na bai daya da za a cimma burin kawo karshen ci gaba da tashe-tashen hankula da ake samu a dukkan jihohin Arewacin Najeriya.
Taron dai ya ‘kara zama wajibi ganin irin yawan mutanen da ake kashewa a jihar Filato, wanda yawansu ya kai 200 ya kuma hada da asarar dukiyoyi da kuma tare matafiya da sauran miyagun ayyuka na ta’addanci dake kawo fargaba.
Babban jami’in hulda da jama’a na ofishin shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, Mallam Mohammad Isah Funtua, yace shugabannin biyu sun ziyarci shugaban kasa domin su jajanta masa tare da yin za’aziyyar abin da ya faru a Jos, lamarin da ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.
Haka kuma shugaba Buhari ya yi musu bayanin abin da ya gani a jihar Filato, da dalilin faruwar abubuwan da kuma bayanan da ya samo daga jami’an tsaron jihar.
Bayan da shugabannin suka kammala tatttaunawa ne shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya wuce zuwa jihar Filato, inda ya gana da gwamna da sauran masu ruwa da tsaki domin neman matakan magance wannan al’amari.
Domin karin bayani saurari rahotan Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5