Sai dai sunayen wadanda suka samu shiga jerin karramawar a bana ya haifar da ce-ce-kuce inda wasu ke ganin da dama ba su cancanta ba yayin da wasu ake gannin sun taka rawar gani a bangori daban-daban na kasar
Wannan dai shi ne karon farko a mulkin shugaba Muhammadu Buhari da aka zakulo 'yan Najeriya da adadinsu ya zarce 400 a lokaci guda wadanda aka karrama da lambar yabo daga bangarori daban-daban na rayuwa kama daga ‘yan siyasa, ma’aikatan gwamnati, ‘yan kasuwa, malamai, jami’an tsaro, manyan lauyoyi, shugabannin gargajiya da na addini har ma da wadanda suka rasa rayukansu
An yi ta muhawarar kan jerin sunayen wasu da a ka gani za su karbi lambar yabon da nuna tababar cancantar wasun su a irin wannan karramawar da ta shafi martabar kasa.
A hirar shi da Muryar Amurka, Adamu Murtala jega mai fashin baki kan al’amuran yau da kullum a Najeriya yana ganin ba’a bi tsarin da ya kamata ba wajen zakulo mutanen da suka yi wa kasa hidima a bangarori da dama.
A nasa bayanin, masani kan kudin tsarin kasa Barrista mai Nasara Umar Kogo ya ce mafi yawan wandanda aka ba lambar yabon, alamu sun yi nuni da cewa mukaminsu aka bi wajen duba cancantarsu musamman wasu 'yan siyasar inda ya ce bai kamata a yi amfani da hakan wajen daidaita ma'auni na siyasa a kasar ba.
Masanin harkokin siyasa a Najeiyar Dakta Faruk BB Faruk na da ra’ayi cewa, shugaban kasar ke da hurumi ya zabi duk wanda ya so kuma dole a mumutunta hakan
Daga cikin wandada aka karrama har da Marigayi tsohon shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin Najeriya Abba Kyari.
Ana dai ba da lambar yabon ne don a yaba da hazakar wasu zababbun ‘yan kasar, wadanda suka yi wa kasa hidima, ta yadda za a iya ganinsu a matsayin jakadun kasa bisa dabi’u da kyawawan ayyuka.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5