Buhari Na Jimamin Rasuwar Dr. Ibrahim Datti Ahmed

Marigayi Datti Ahmed

Wani dattijo kuma Shugaban Majalisar Koli ta Shari'a a Najeriya (SCSN), Dr Datti Ibrahim Ahmed, ya rasu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna juyayi bisa rasuwar tsohon shugaban majalisar koli ta shari'a a Najeriya, Dr. Ibrahim Datti Ahmed.

Shugaban kasar a cikin ta'aziyyar tunawa da marigayin wanda likita kuma dan siyasa wanda ya taba tsayawa takarar shugaban kasa, ya bayyana tsohon shugaban majalisar koli ta shari'an Najeriya a matsayin n mutum mai albarka da tarin hikima.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da kakakin shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya fitar.

Marigayi Datti ya rasu da sanyin safiyar Alhamis a jihar Kano. Shekarunsa 83.

Dr. Datti ya taba tsayawa takarar shugaban kasa.

Marigayi Ahmed ya rasu ya bar mata daya da ‘ya’ya 10. Tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.